An karɓo daga Abu Abdurrahman Abdullahi ɗan Mas'ud (R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ba mu Iabari, shi ne mai gaskiya cikin dukkan al'amuran da yake, kuma abin gasgatawa, ya ce, "Lallai kowane ɗayanku ana tara halittarsa a cikin mahaifiyarsa, tsawon kwana arba'in yana maniyyi, sannan ya canza ya zama gudan jini kwatankwacin wannan, sannan ya juya ya zama tsoka kwatankwacin haka, sai a aiko Mala'ika ya busa masa rai, a umarce shi da rubuta kalmomi huɗu: A rubuta arziƙinsa da ajalinsa, da aiyukansa, da kuma, ɗan wuta ne ko aljanna. Na rantse da wanda babu wani abin bauta sai shi, lallai ɗayanku zai yi aiki irin na 'yan aljanna, har ya zamanto ba abin da ke tsakaninsa da aljanna sai zira'i ɗaya, sai rubutun can ya rigaye shi, sai ya yi aiki irin na 'yan wuta, sai ya shige ta. Lallai ɗayanku da zai yi aiki irin aikin 'yan wuta, har ba abin da ke tsakaninsa da ita sai zira'i ɗaya, sai littafi ya rigaye shi, sai ya yi aiki irin aikin 'yan aljanna, sai ya shige ta. Bukhari (#3208) Muslim #2643).
SHARHI
Abdullahi bin Mas'ud (R.A) yana cikin
sahabban farko da suka musulunta kuma suka yi hijira. Shi mutum ne wanda yake mai ƙaramar halitta, har wata rana ya hau kan wata itaciya, sai sahabbai suke dariya saboda ga shi gajere, ga kuma ƙwaurinsa
siriri, sai Annabi (ﷺ) ya ce da su, ”Yanzu ƙwaurin Abdullahi ɗan Mas'ud kuke yi wa dariya, na rantse da wanda ran Annabi
Muhammad (ﷺ) yake hannunsa, ƙwaurin nasa guda biyu in an ɗora a kan mizani, sun fi ƙarfin dutsen Uhudu." [Imam Ahmad ne ya rawaito shi] Shi ne mutumin da Annabi (ﷺ) ya ce, "Karanta min Alkur‘ani!" Sai Abdullahi ɗan Mas'ud ya ce, "Ai kai aka saukarwa.”, sai ya ce, "Ni aka saukarwa, amma ina so in ji daga bakin wanina. Karanta min in ji." Sai ya karanta masa suratun Nisa'i har zuwa wajen faɗin Allah,
(Yaya matsayin mutane zai zama. idan muka zoda kowace al’umma tare da mai yi mata shaida, kai kuma mu zo da kai kana mai yin shaida kan wannan al’ummar?) [Annisa'i 41] [Bukhari (#4582) da Muslim (#800) suka rawaito shi]
Abin da ake nufida cewa, "....sai littafinsa ya rinjaye shi....", shi ne sai rubutun can da aka yi tun yana ciki, sai ya rinjaye shi, sai ya zo ya yi aikin da shi aka rubuta, sai ya shiga cikin masu irin wannan aikin. Abin da wannan hadisi ke nunawa, idan ka gan ka a ayyukan ɗa‘a, kana aiki na ɗa'a, ka roƙi Allah ɗorewa har zuwa mutuwa a kan wannan aikin, don ba ka san ƙarshen rayuwa ba.
Kullum ba farkon ba, ƙarshen! Wannan ya sa Annabi (ﷺ) yake cewa, "Ya Allah mai jujjuya zukata! Tabbatar da zuciyata a kan addininka." [Tirmizi ya rawaito shi (#2140) da Imam Ahmad]. Saboda haka
kullum ka gan ka a cikin alheri, sai ka rinƙa yi wa kanka addu'a a cikin dare. Sannan kuma idan mutum ya yi aikin ɓarna, kar ya ɗebe tsammani ya ce, to ai yanzu ni da na yi aikin ɓarna iri kaza, watakila ko na tuba ba za a karba ba. Allah ya ce,
(Ka ce, "Ya ku bayina waɗanda suka yi wa kansu ɓarna! Kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Haƙiƙa Allah yana gafarta zunubai gaba ɗaya. Haƙiƙa Shi (Allah) mai yawan gafara ne mai jin ƙai") [Azzuman 53]
Don haka ba a so ka ɗebe tsammani, duk yawan zunubanka in ka tuba, Allah zai gafarta maka. Zunubi na ƙarshe shi ne shirka, amma idan mutum ya tuba Allah zai canza munanan ayyukansa, su zamanto kyawawa. Wannan hadisi abin da yake nunawa kenan.
Waɗansu kuma suka zo wajen Annabi (ﷺ)
suka ce da shi, in dai ya zamanto an rubuta komai tun mutum na ciki, to me ya sa za a sa mu yi aiki? A Kyale mu, mu tsaya a kan rubutun da aka yi tun muna ciki mama! Sai Annabi (ﷺ) ya ce, "Ku yi aiki kowanne da sannu za a karkatar da shi zuwa ga abin da aka rubuta shi a kai." [Duba Bukhari (#6217) Muslim (#2647)]. Saboda haka, za ka kafa hujja ne da abin da Allah ya ce, ba abin da Allah ya rubuta ba, don abin da ya rubuta ya riga ya rubuta, amma bai faɗa maka a inda ya rubuta ka ba? Amma a Alƙur'ani mai girma ya ce, ka yi sallah, ka yi zakka, ka yi imani, ka kyautata wa iyaye. To sai ka bi wannan umamin na Alkur‘ani, don shi ne tabbas, don waccan rubutun, ba ka san inda aka rubuta ba.
Haka nan wannan hadisi yana nuna matakan halittar dan Adam: Matakin farko, digon maniyyi; mataki na biyu ya zamagudan jini; sannan kuma ya zama tsoka; sannan a busa rai. Matakai guda hudu kenan! Wannan yana nuna cewa ɗan Adam a ciki, ba ya zama ɗan Adam, sai ya kai wata huɗu, sannan yake zama zan Adam, amma a wancan lokacin, duk waɗansu zango ne na ɗaya da na biyu da na uku, wanda ba a riga an busa rai ba.
Shi ya sa malaman fiƙihu suke bayani dangane da wanda ya yi yunƙurin zubarwa da mace cikinta, ko ya doke ta, har cikinta ya zube. Akwai fatawarsu, in ba a kai wata huɗu ba, akwai kuma fatawarsu, in an kai wata huɗu. Saboda in ba a kai wata huɗu ba, bai riga ya zama rai ba, in an kai wata huɗu, ya riga ya zama rai. Sai dai akwai hadisi a cikin sahihu Muslim [#2645] wanda ke nuna a cikin arba'in ta biyu, Ubangiji yana umartar Mala'ika ya sawwara halittar ɗn Adam. To yaya za a yi a haɗa su? Sai waɗansu suka ce, ai can taswiri aka ce, babu busa rai, taswiri daban, busa rai daban.
A waɗansu ayoyin, sai aka nuna matakai guda bakwai ake bi, wasu kuma suna nuna guda biyar, a ƙarshe za ka ga sun kai guda bakwai, Allah ya ce;
(Haƙiƙa mun halicci mutum daga tsantsar taɓo. Sannan muka sanya shi digon maniyyi a cikin wata matabbata amintacciya. Sannan muka halicci digon maniyyin nan ya zama gudan jini, sai muka halicci daga gudan jinin nan tsoka, daga tsokar nan sai muka halicci ƙashi, sannan muka lulluɓe ƙashin da nama, sannan muka samar da shi a wata halitta daban. Albarkar Allah wanda ya fi kowa iya halitta ta yawaita) [Almu‘uminun 12-14] Mataki bakwai kenan!
Wannan hadisi ya kawo guda huɗu, ashe sai ka ɗauki nan ka ɗauki can, sannan sai ka haɗa ɗan Adam gaba ɗaya. In ka ɗauki wuri ɗaya ba za ka iya haɗawa ba.

Allah yabada lada
ReplyDeleteAllah ya kara ilimi da basira tare da kyautar Aljannatul-Firdaus, Aameen! ~I_M_Kauji
ReplyDelete