Neman Tsarin Wanin Allah Shirka Ne
Da faɗin
Allah:
"Lallai daga cikin mazaje na mutane, akwai waɗanda
suke neman kariya ko tsari daga wurin mazaje na aljanu. Sai suka kara musu (aljanu)
shisshigi da girman kai." (Al-Jinn: 6)
______________
SHARHI
Abin da malaman tafsiri suke faɗa shi ne Larabawa a jahiliyyarsu, idan suka yi tafiya, suka isa masauki, don jin tsoron kada wani abu ya same su, ko dawakansu, ko raƙumansu, sai su ce suna neman tsari da shugaban wannan wuri, ya kare su daga dukkan mai cutarwa a wannan wajen. Suna nufin shugaban aljanun wajen ya kare su daga
sauran aljanun wajen.Wannan ya sa sarkin aljanun wajen, sai ya riƙa cewa, "Ashe
bayan aljanu ma, mutane na tsoro na." Sai wannan ya ƙara masa girman kai.
Ka ga a nan Ubangiji ya kawo wannan aya da ba da labarin waɗansu
mutane da ke neman tsarin aljan.
Ya uuzuna: Isti'aza ibada ce, don haka ba a
nemanta sai a wurin Allah. Shi ne Ibn Kathir yake cewa, ayoyi ne 3 ba su da na
4 cikin Alkur'ani da suke nuna haka. Akwai kangararrun shaiɗan,
akwai na bil Adama. Kangararrun bil Adama, mai munin hali, yadda za ka magance mummunan
halinsa, shi ne ka yi masa ɗabi'a
kyakkyawa. Idan ya yi maka rowa, sai ka yi masa kyauta, in dai yana nan bai
canza ba, to dole zai
sauko. Amma kangararren shaiɗan
kuwa, babu yadda za ka yi da shi, wannan sai dai ka nemi tsarin Allah da shi.
Wannan ya nuna ibada ce Isti'aza. Don haka, dole a nemi tsari a wurin Allah, in
dai aka nema wurin aljan, mala'ika, Annabi, ko shaihi, ko wani waliyyi, to an yi
shirka. Duk wanda za ka nemi ya kare ka daga abin da kake jin tsoro, to wannan
din bawa yake ga Allah. Kuma Allah (SWA) ya yi umarni da isti'aza, kamar yadda
ya yi umarni da sallah. Ƙololuwar
martaba kafin ka ambaci sauran Annabawa da mala'iku, bayi ne kuma mabukata ne
wurin Allah (SWA). Su kansu Annabawa ba su nemi tsari ga kansu ba, sai ga
Allah. Annabi Nuhu (AWS) ya nemi tsari ga Allah;
Ya ce 'Ya Ubangjina lalle ne ni ina neman tsari
gare ka, kada in tambaye ka abin da ba ni da wani ilimi a kansa. Idan ba ka
gafarta mini ba, kuma ka yi mini rahama, zan kasance daga masu hasara."
(Hud:47)
Sakamakon da Allah ya yi masa saboda isti'azarsa,
shi ne aka yi sakamakon da ya shafi jama'arsa:
"Aka ce da Nuh, sauka cikin jirgi cike da
aminci (babu jin tsoro); da albarkatai masu tarin yawa gare ka, har waɗanda
suke tare da kai (cikin jirgin), har waɗanda
za su biyo baya." (Hud:48)
Annabi Yusuf (ASW) lokacin da matar nan ta nemi ya
aikata alfasha da ita, cewa ya yi, Ina neman tsari ga Allah!" Sai Allah
(SWA) ya yi masa sakamako da Burhani.
Mahaifiyar Annabi Isa (ASW), lokacin da mala'ika
Jibril (ASW) ya zo wurinta, isti'aza ta yi. Da ta yi haka, sai aka ba ta ɗa.
Ba wai kyautar ɗan ne ya fi daɗi
ba, ɗan ya yi magana yana jariri. Don, idan
an ba ta ɗan bai yi magana ba, za a tuhumce ta
da zina. Lókacin da ta zo da shi, sai suka tambaye ta ina ta samo ɗa?
Sai ta nuna shi. Suka ce, "Yaya za a yi mu yi magana da jariri?" Sai
ya yi magana. Ba wai barrantar da ita kaɗai
ya yi ba, sai ma da ya ƙara
ba su labarin shi manzo ne. Ka ga sakamakon
Isti'aza kenan. Annabi ( SAW) ma an umarce shi da
yin isti'aza. Ka dubi Suuratul Falak da Naas. Don a nuna babu wanda ya cancanta
a yi isti'aza da sunansa, sai Rabbil Falak, sai Rabbin-Naas. To, wanene a cikin
mala'ika ko Annabi zai zama Rabbil Falak ko
Rabbin-Naas ?
********************************************
An karɓo
hadisi daga Khaulatu 'yar Hakim (RA), ta ce, "Na ji Manzon Allah (SAW)
yana cewa, "Wanda duk ya sauka a wani masauki, sai ya ce, (A uzu bi
kalimatul-lahit-tammati min sharri ma Khalaƙ ina neman kariya da kalmomin Allah
cikakku daga sharrin abin halitta (ma'abocin sharri). Duk wanda ya faɗi
haka babu abin da
zai cutar da shi har sai ya bar wurin ya ci
gaba." [Muslim #27008]
________________
SHARHI
Haulatu bintu Hakim: Ita ce matar da ta zo ta
gabatar da kanta wurin Manzon Allah (SAW) ta ce, ""Na ba ka kaina."
Sai Manzon Allah (SAW) ya yi shiru bai ce komai ba, sai wani sahabi ya ce da
Manzon Allah (SAW), "Ya
Rasulullah! Idan ba ka da buƙata, mu muna da buƙata." Sai Annabi
ya ce.
"Ka kawo sadaki." Ya ce, ba shi da
komai. Sai Annabi ya sake cewa, "Ka je ka bincika." Sai ya dawo ya ce
ba shi da komai sai mayafinsa. Sai Annabi ya ce, "Ka haddace wani abu daga
Alƙur'ani?
Ya ce, "Eh!" Sai Annabi ya ce da shi, "Ka je ka karantar da ita.
Wannan shi ne sadakinka."(Bukhari)
A uzu bi kalimatul-lahit-tamati min sharí ma khalaƙ:
muna neman tsari da kalmomin Allah cikakku? Shi ne
malamai suka ce, kalmomin Allah su ne maganar Allah, kuma maganar Allah siffa
ce daga cikin sifofinsa. Idan ka nemi tsari daga maganar Allah, ka nemi tsarī
ga Allah (SWA) kenan. Ma'anar cikakku wato, duk inda kalmar Allah take, cikakkiya
ce. Kasancewar maganar Allah duk inda ya faɗa
ba ya sabawa, shi ya sa ta zama cikakkiya kenan. Amma akwai ruwaya cikin
Bukhari, wanda Sheikh Muhammad ibn Abdulwahab ya kamata a ce ya gabatar da ita.
Bisa ka'ida, idan hadisi Bukhari da Muslim sun kawo shi, kamata ya yi a fara
gabatar da na Bukhari. Hadisin da ke cikin Bukhari [#3371] na Abdullahi ibn
Abbas ne, ya ce, Annabi (SAW) ya kasance yana yi wa Hassan da Hussain isti
'aza, sai ya ce da su, "Kakanku Ibrahim ya kasance yana yin isti'aza ga
'ya'yansa guda biyu, Isma'il da Ishaƙ. Abin da yake cewa
kuwa, A 'uzu bi kalimatullahit-taammati min kulli
shaiɗanin wa hamma, wa min kulli ainin
lammat. "Wato, ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga dukkan wani
shaiɗan ma'abocin dafi da mai kambun
bakan da ke nufatar mutum da sharri.
Mahalush-shahid a nan, shi ne Annabi (SAW) ya ba da umarnin cewa a nemi tsari
ga Allah da kalmomin Allah cikakku, wato maganganun Allah (SWA) kenan. Alƙur'ani na cikinsu
da duk wata magana da Allah ya yi, za ka karanta
ne babu adadi, ko sau nawa ka faɗa
ya yi. Domin abin da Annabi (SAW) bai iyakance masa adadi ba, to ba a yi masa
iyaka, kuma abin da ya iyakance, ba a kara masa.
********************************************
A
Cikin Wannan Babi Akwai Mas'aloli Kamar Haka:
1. Tafsirin ayar Suuratul Jinn.
2. Neman tsari ga wani ba Allah ba, shirka ne.
3. Kafa hujja da wannan hadisin Annabi. Domin
malaman suna kafa hujja da hadisin cewa kalmomin Allah ba halitta ba ne (sifa
ce daga cikin sifofinsa), suka ce (in da maganar Allah halitta ce), to idan aka
nemi tsari da halitta, kuma wannan shirka ne.
4. Falalar wannan addu'ar duk da cewa gajeriya ce.
5. Kasancewar abu ana iya samun amfanin duniya,
wajen kare sharri ko jawo amfani, wannan ba ya nuna cewa ba shirka ba ne.
(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ). (zamuci gaba Insha Allah)
No comments:
Post a Comment