Yana Daga Shirka Neman Taimakon Wanin Allah Ko Roƙon Wanin Allah
________________
SHARHI
Mun riga mun san duk
wani nau'in ibada da ake yi wa Allah (SWA), to idan a ka yi wa wani ba Allah
ba, to ya zama shirka kenan. A nan Malam ya ce neman tsari wato istigatha"
da wanin Allah shirka ne, kenan istigatha' ibada ne wanda ba wanda za a yi wa
sai Allah. Kuma kamar yadda Allah ya yi umarni da sallah haka ya yi umarni da
istigatha'wato neman tsari, kamar yadda ya ce:
"Idan wani mai
zungura daga shaiɗan ya zungureka to ka nemi tsari daga wajen Allah, haƙiƙa shi
(Allah) mai ji ne kuma masani." (Fussilat:36)
Don haka neman tsari ibada ce ba a yi da kowa
sai Allah (SWA). Idan aka nema a wajen wani waliyyi, ko Annabi, ko mala'ika ko aljani to duk an nema wajen wanin Allah, duk an yi shirka. Da mala'iku da Annabawa dukkansu bayi ne na Allah, ayoyi da dama sun tabbatar da haka. Tunda bayi ne su to, suna neman buƙata wajen Allah. Su kansu Annabawa neman tsari da Allah suke yi, ba sa yi da kansu. Annabi Nuhu (ASW) ya nemi tsarin Allah a cikin Suuratul Hud, Allah ya tserar da shi da wadanda suke jirgin ruwa tare da shi albarkacin neman tsarin Allah da ya yi. Haka Annabi Yusuf (ASW) ya nemi tsarin Allah da matar sarki ta neme shi kamaryadda ya zo cikin
Suuratul Yuusuf Haka mahaifiyar Annabi Isa (ASW) Nana Maryam ta nemi tsari da
Allah lokacin da mala'ika ya zo mata. To Annabi (SAW) an umarce shi da
istigatha a cikin Suuratul Falaƙi da Naas.
Shi ne Ibnul Ƙayyim
yake cewa rukunan istagatha'guda uku ne.
a. Abin neman tsarin wato
Allah (SWA) kenan kamar yadda muka tabbatar shi kaɗai ne,
b. Abin sharrin da ake
neman tsarin Allah daga gare shi, waɗannan su ne abubuwan nan hudu wanda
Suuratul Falaki ta yi bayaninsu kamar haka:
Ka ce, Ina neman tsari
a wajen Ubangijin safiya. Daga sharrin
abin da ya halitta
(ma'abocin sharri), kuma daga sharrin dare,
idan ya yi ɗuhu. Kuma
daga sharrin masu tofi a cikin ƙulle-
ƙulle. Kuma daga
sharrin mai hassada, idan zai yi hassada."
(Falaƙ:1-5)
Dukkan wani abin sharri
yana cikinsu. Na farko tsari daga
dukkan abin da Allah ya
halitta na sharri, ba za ka ce dukkan
abin da Allah ya
halitta ba, saboda ba duk halittarsa ba ce take da sharri, kamar aljanna ba
sharri a cikinta. Sai na biyu, dare idan duhunsa ya zo. Aljanu karfinsu ya fi
da daddare a kan rana, sannan an fi jin tsoro da daddare a kan rana. Sai na uku
masu tofi cikin ƙulle-ƙulle wato masu tsafi kenan da masu
sihiri. Sai na huɗu mai
hassada yayin da zai yi hassadar.
c. Sai na uku shi ne
lafazin da manzon Allah ya yi amfani da shi wajen neman tsarin.
****************************************
Da faɗar Allah:
"Kada ka roƙi
wanin Allah abin da ba ya iya amfanar da kai ko cutar da kai. Idan ka aikata
haka, to ka shiga cikin azzalumai (ka zamanto cikin masu shirka kenan.) Idan
Allah ya shafe ka da wata cutarwa, babu mai yaye maka (cutar) sai Allah. Idan
kuma Allah ya nuface ka da wani alheri, babu wanda ya isa ya juyar da alherin.
Ubangiji na isar da alherinsa ga wanda ya so cikin bayinsa. Domin shi mai
gafara ne mai jinkai."(Yunus 106-107)
____________________
SHARHI
Wannan ayar tana nuna
mana cewa ba wanda yake cuta ko amfanarwa sai Allah (SWA), haka Allah ya umarci
Annabi da ya yi shela ya faɗa:
"Ka ce, Ni fa ba
zan iya mallaka muku wata cutarwa ko kuma shiriya ba Ka ce, "Ba fa wani
wanda ya isa ya tserar da ni daga Allah, kuma ba zan taba samun wata mafaka ba,
in ba a wurinsa ba." (Jinn:21-22)
To idan har Annabi ba
shi da mukullan, to ba yadda za a yi a samu a hannun wani. Shi ya sa Allah
(SWA) ya ce idan har ka aikata haka to ka shiga cikin azzalumai. A nan kuma
zalunci yana nufin kafirci. To Allah ya ce kar ka kira wani ba Allah ba, ko
mala'ika ne, ko Annabi ne, ko aljani ne, in dai ba Allah ba ne to ba ya halatta
ka kirawo shi domin ya amfanar da kai ko ya kare ka daga masifa. Wannan maganar
Allah ya fuskantar da ita zuwa ga annabinsa amma abin nufi shi ne zuwa
daidaikun al'umarsa tun da Allah ya san annabinsa ba zai yi shirka ba. An
jigina magana zuwa gare shi don mu ta tsoratar da mu kwarai da gaske. Don haka
kiran wani ba Allah ba, ɗaukar wani haƙƙi ne na Allah kaɗai, ka ba wa wanin Allah,
wannan babban zalunci ne da ba sama da shi.
****************************
Da faɗinsa:
"Ku nemi arziƙi a
wurin Allah kaɗai, kuma ku bauta masa, kuma ku gode masa, gare shi za ku
koma." (Al-Ankabuut: 17)
_______________________
SHARHI
Ayar ta zo cikin ƙissar
Annabi Ibrahim (ASW) cikin Suuratul Ankabul Allah (SWA) cewa ya yi, "Ku
nemi arziƙi wajen Allah kaɗai." Wato wan bai shigo ciki ba. Amma da cewa
aka yi, "Ku nemi arziki wajen Allah wannan bai hana ku nema wajen waninsa
ba.
******************************
Da faɗinsa:
"Babu wanda ya fi
kowa ɓata, sama da wanda yake kiran wanin Allah, wanda ba zai taɓa amsa masa ba
har zuwa ranar alƙiyama, Kuma su (waɗanda aka kira) dangane da kiran, gafalallu
ne (wato ba su san anyi ba)
_________________
SHARHI
Ƙarshen ayar shi ne:
Idan an tara mutane za
su kasance maƙiya gare su kuma za su kafircewa ibadunsu."(Al-Ahkaaf:6)
A ranar kiyama waɗanda
suka ɓatar da mutane za su yi tawaye da mutanen da suka ɓatar. Suna cewa
mabiyansu sam ba mu yarda da ibadar da kuka yi mana ba, mu ba mu ce ku bautata
mana ba, ba mu ce ku roƙe mu ba, ba mu da komai, matattu muke, me ya sa kuka
roƙe mu? Wallahi
sai sun faɗi haka ranar
tashin ƙiyama! Haka Allah ya kawo wannan ƙissar a cikin ayoyi daban-daban a
Alƙur'ani:
Tuna (abin da zai faru)
lokacin da waɗanda aka yi wa biyayya, suka barranta daga waɗanda suka yi musu
biyayya, (bayan) sun ga azaba, sai dukkan wata dangantaka (da take a
tsakaninsu) ta yanke. Kuma waɗanda suka yi biyayyar za su riƙa cewa, "Ina
ma muna da damar (a mayar da mu
Duniya), mu ma mu
barranta daga gare su (a duniya), kamar yadda suka barranta daga gare mu (a
yau)?" Kamar haka ne Allah zai nuna musu ayyukan su, (a matsayin) abin yin
nadama gare su. Da ɗai, ba za su zamo masu fita daga cikin wuta ba."
(Al-Baƙara:166-167)
Waɗanda aka bi za su
barranta daga waɗanda suka bi su don sun ga azaba ƙiri da muzu, sannan dukkan
wani sababi da aka sa na kusa wane muridi ne, duk za su yanke a ranar. Su kuma
mabiya za su ce ina ma a mai samu duniya
mu yi musu tawaye kamar yadda su wane suka yi ta wayen tun a duniyar, mu
ma mu yi musu tawaye tun da yau su ma sun yi mana tawayen. Sai Allah ya ce haka
za mu nuna musu aikin su abin damuwa abin baƙin ciki.
A wani wajen Allah
(SWA) yake ba da labari, idan an wulla mabiya cikin wuta sai su nuna shugabanni
su ce ya Allah waɗannan su suka ɓatar da mu, ninka musu azabar wuta su ne
manyan masu laifin. Sai Allah (SWA) ya ce "kowa sai an ninka masa."
Don haka duk wanda za ka bi ka tabbatar
ya sa ka bin Allah da
Annabi (SAW). Duk wanda ya ce ma rufe ido ka bi ni kar ka yarda. Don babu
tsoron Allah a wajen dan bidi'a, abin da yake kallo kawai duniyarsa, ya za a yi
ya kare matsayinsa. Masu sufancin da, su suka gina sufancinsu a kan tsoron
Allah. Amma sufayan yanzu galibin su karya suke. Sufayen da, irinsu Sahal ibn
Abdullahi Tusturi, irinsu
Junaid ibn Muhammad
Alkawariri, irinsu Shehu Abdulkadir Aljilani waɗannan duk da gaske suke,
tarihinsu da maganganunsu da ayyukansu duk ya nuna da gaske suke yi. Amma
sufayen karshen zamani ba wanda yake da gaske cikinsu, ba wanda yake kira kan
bin tafarkin Manzon Allah. Suna fakewa ne da Annabi don a bi su su gina kansu.
********************************
Da faɗinsa
"Shin wanene yake
amsawa wanda yake cikin matsí idan ya kira shi.
kuma ya yaye
cuta?"(An-Naml 62)
_______________
SHARHI
Duk waɗannan ayoyin
suna nuna cewa, ba za a nemi taimakon kowa ba, ko a nemi kariyarsa, in ba Allah
(SWA) ba.
********************************
Ɗabarani [Ahmad J5/317]
yaruwaito hadisi da sanadinsa
cewa, akwai wani
munafuki lokacin Annabí (SAW) wanda yake cutar da muminai. Sai wani sashi na
muminai suka ce, "Mu tafi wurin Manzon Allah, mu nemi taimakonsa don ya
kare mu daga sharrin wannan munafukin." Sai ya ce, "Ai ba a neman
agaji da ni, sai dai a wurin Allah."
_______________________
SHARHI
Wannan hadisi mai rauni
ne, amma hukuncin ciki ya tabbata a ayoyın da suka gabata.
**********************************************
A Cikin Wannan Babi Akwai Mas'aloli Kamar Haka:
1. Kawo addu'a bayan an
kawo maganar neman taimako, yana
cikin babin ambaton
gamammen abu, bayan an ambaci
keɓantacce.
2. Tafsirin ayar
"Kada ka roƙi wanin Allah...."
3. Kiran wanin Allah
babbar shirka ce.
4, Mafi nagarta a cikin
mutane da a ce zai aikata kuma ya yarda da hakan (kiran wanin Allah), da zai
zamanto cikin
azzalumai.
5. Tafsirin ayar da ta
biyo bayan wannan.
6. Kasancewar (kiran
wanin Allah) ba ya amfani a duniya, tare
da kasancewar hakan
kafirci ne.
7. Tafsirin aya ta uku.
8. Neman arziki ba ya
dacewa, sai wurin Allah kaɗai kamar
yadda Aljanna ba a
nemanta sai wurinsa.
9. Tafsirin aya ta
hudu.
10. Babu wani mafi bata
(a ban-kasa) sai wanda ya kira wanin
Allah.
11. Shi wanda ake kira
gafalalle ne ga kiran mai kira ɗin, bai san yana yi ba.
12. Kiran wani wanda ba
Allah ba, zai sanya ƙiyayya ga wanda
ake kira (a gobe
ƙiyama).
13. Yadda aka ambaci
kiran wanin Allah da cewa ibada ne ga
wanda aka kira din.
14. Wanda ake kira zai
bijire wa wannan kiran (da aka yi masa a gobe ƙiyama). Waɗannan al'amura (da
aka ambata) su ne suke sanya wanda ya kira wanin Allah ya zamanto mafi ɓata
daga mutane.
16. Tafsirin aya ta
biyar
17, Wani al'amari mai
ban mamaki shi ne ta yadda ko da
waɗanda suke bautar
gumaka, sun yi iƙirari cewa babu mai
amsa wa wanda yake
cikin tsanani sai Allah. Don haka
suke kiran Allah idan
suna cikin tsanani.
18. Yadda Annabi (SAW)
yake ba da kariya game da bangon
tauhidi da kuma yadda
ladabinsa yake game da Ubangiji.
No comments:
Post a Comment