Yin Bakance Don Wanin Allah Shirka Ne
Da fadin Allah;
"(Muminai nagari) suna cika bakance..(¹)
"(Al-Insaan :7)
____________________
SHARHI
Wannan ayar ta nuna bakance ibada ce. In kuwa ibada ce, yin ta ga wanin Allah ya zama
shirka kenan.********************************************
Da fadinsa;
"Lallai duk abin da za ku ciyar na daga
ciyarwa, ko abin da kuka yi
bakance na daga dangin bakance, to lallai Ubangiji
ya san kun yi... (²) (A-Bakara:270)
____________________
SHARHI
Shi ne Ibn Kathir yake cewa, a cikin wannan ayar
akwai alƙawari
na sa rai, sannan akwai alƙawari
na firgici, wato waɗanda suka yi ciyarwa
ko cika bakance da kyakkyawar niyya, to Allah (SWA) ya san da abin, zai ba su lada.
Sannan kuma razani da firgici ga waɗanda
suka yi ciyarwar ko cika bakancen nan domin wanin Allah, to Allah ya san da
abin, kuma zai musu mummunan sakamako a kai.
***********************************************
Ya tabbata cikin Sahihul Bukhari, an karɓo
hadisi daga Aisha (RA), Annabi (SAW) ya ce, "Wanda ya yi bakancen biyayya
ga Allah, to lallai ya bi shi, wanda kuma ya yi bakance zai saɓa
wa Allah, to kada ya yi." [Bukhari #6696, Abu Dawud#3289, Timizi #1526]
_____________________
SHARHI
Ta yaya bakance zai zama na sabo? Ko dai mutum ya
yi bakance don wanin Allah, ko kuma ya yi bakance don Allah, amma wurin cika bakancen
ana saɓa wa Allah. A irin wannan, dole ne
cika bakance, amma sai dai ba zai cika shi a wannan wurin ba. Don cika shi a
wurin ya zama saɓo kenan. Duk wanda ya
yi bakance na saɓo, ba zai cika shi
ba, to wannan bakancen ya zama ba shi, sai dai zai yi kaffarar rantsuwa.
******************************************
A
Cikin Wannan Babi Akwai Mas'aloli Kamar Haka:
1. Wajabcin cika bakance, (idan ba saɓon
Allah ba ne).
2. Idan bakance ya kasance ibada ce, to juyar da
shi ga wanin Allah ya zama shirka.
3. Bakancen da aka yi wanda ya ƙunshi saɓo,
ba ya halatta a cika shi.
(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ). (zamuci gaba Insha Allah)
No comments:
Post a Comment