SHARHI
Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga
dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka dalilan
da suke nuna cancantar Allah da bauta shi kaɗai,
Da kuma dalilan
da ke nuna kasawar wanin Allah wajen a bauta masa.
Zai kawo siffofi da suke nuna cancantar Allah a bauta masa shi kaɗai
da siffofi da suke nuna duk wanda ba Allah ba, yana da rauni bai dace a bauta
masa ba. Abin da wannan babi da mai bi masa za su nuna mana kenan.
************************
Da faɗin
Allah;
Shin suna haɗa Allah da wani, wanda ba ya halittar komai, alhalin su ne ake halittawa. Kuma ba sa iya taimaka musu, kuma ko da kawunansu ba sa iya taimakawa? (Al-Araaf 191-192)