Jin Tsoron Afkawa Cikin
Shirka
______________
Wannan babi zai yi
magana a kan jin tsoron afkawa cikin shirka. Wato alamar imani ya kankama a
jikin mutum shi ne kullum ya ji yana tsoron afkawa cikin shirka, mutum yana
taka-tsantsan a magana ko aikin da yake shirka ne. Kar mutum ya amintu ya dinga
jin cewa ya tsira ya hau tudun mun tsira daga afkawa cikin shirka.
********************
Da faɗin Allah;
“Haƙiƙa Allah ba ya
gafarta wa haɗa shi da wani (shirka), yana gafarta wa abin da bai kai shirka
ba, ga wanda ya so. (An-Nisaa:116)
________________
SHARHI;
Wannan aya ta maimaitu
har sau biyu a Suuratul Nisaa’i. Menene shirka? Abin da ake nufi da shirka, shi
ne kamanta abin halitta da mahalicci.