Falalar Tauhidi Da
Yadda Yake Kankare Zunubai
Da fadin Allah;
”Waɗanda suka yi imani, ba su garwaya imaninsu
da zalunci ba, lallai su ne suke da amintuwa, kuma su ne shiryayyu.” (An'aam:
82)
_________________
SHARHI;
Wannan aya ta zo a
daidai inda aka ba da ƙissar Annabi Ibrahim (AS) na muƙabala da ya yi da
mutanensa da hana su bautar gumaka, sai ake tambaya cewa, da su mushirikan da
Annabi Ibrahim waye a kan shiriya?
Sai Allah ya ba da amsa
a Wannan ayar.
Idan an ce,