KITABUT-TAUHID
_____________
SHARHI
Abin da tauhidi yake
nufi shi ne kaɗaitawa, Wato daga Kalmar wahhada, Malam a nan ya na nufin
Kitabut-tauhidillahi wato llttafin kaɗaita Allah. Kaɗaita Allah, kuma
ta ɓangarori ne guda
uku.
1) Rubuubiyya: Daga kalmar Rabb, wadda
ma’anarta shl ne mai halitta da kuma kulawa da halitta ɗin. Tabbatarwa da Allah
(SWA) ne kadai ya yi halittu gabaɗaya kuma yake kula da su, shi ne kaɗaita
Allah da rububiyya.
2) Uluuhiyya ko Al-Ilahiya: Daga kalmar A
I-ilaallu wato alma ’abuudu wato abin bauta. Amma a shari’a ldan an ce
alma’abuudu abin da ake nufi shi ne abin bautawa bautar ta gaske,
Don haka duk wanda aka
bautawa ba Allah ba, to ba bautar gaske ba ce. Allah (SWA) kaɗai ake wa ta
gaskiya. Shi ya sa kalmar shahada ta ƙunshi ɓangarori guda biyu: Bangare na
farko, kwaɓe rigar ilahantaka ga kowa wato Iaa ilaaha. Sal kuma Bangare na biyu
illallahu, wato sal Allah (ﷺ) kaɗai.
3) Kaɗaita Allah wajen sunayensa da siffofinsa.
Dukkan suna ko siffa na Allah, nasa ne, wani ba ya tarayya da shi wajen sunan
ko siffar.
********************
Da faɗin Allah Ta’ala;
"Kuma ban halicci
aljanu da mutane ba, sai domin su bauta mini." (Zaariyaa; 56)
__________________________
SHARHI
Malam da ya ce
Kitabut-tauhid, sai ya fara da kawo ayoyi da hadisai. Wato ba ra’ayinsa ya kawo
ba, zallar gaskiya ce.
Kalmar ‘aljanu’ a ayar ta haɗa