GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Aug 6, 2010

ARBA'UNA HADITH {2} HADISI NA BIYU

An karɓo daga Umar (R.A) ya ce, "Yayin da muna zaune a wurin Annabi (ﷺ) wata rana, sai wani mutum ya bayyana gare mu, mai tsananin farin tufafi, mai tsananin baƙin gashi, kuma ba a ganin alamun tatiya tare da shi, kuma a cikinmu babu wanda ya san shi, har ya zauna kusa da Annabi (ﷺ) ya jingina gwiwowinsa guda biyu zuwa ga gwiwowin Annabi (ﷺ), ya ɗora tafukan hannunsa a kan cinyoyinsa, sai ya ce, "Ya Muhammad! Ba ni labari game da musulunci." Sai Annabi (ﷺ) ya ce, "Muslunci, shi ne ka shaida babu abin bautawa bisa ga cancanta, sai Allah, kuma Muhammad  (ﷺ) Manzon Allah ne, ka tsayar da sallah, ka ba da zakka, ka yi azumin watan Ramadan, ka ziyarci ɗakin Allah in ka sami iko." Sai ya ce, "Ka yi gaskiya!" Sai muka yi mamakinsa, saboda yana tambayarsa, kuma yana gasgata shi. Sai ya ce, "Ba ni labarin Imani." Sai ya ce, "Ka yi imani da Allah, da Mala'ikunsa da Littattafansa, da Manzanninsa da ranar lahira, kuma ka yi imani da ƙaddara alherinta da sharrinta." Sai ya ce, "Ka yi gaskiya!" Sai ya ce, "Ba ni labarin kyautatawa." Ya ce, "Ka bauta wa Allah kamar kana ganinsa, idan ba kaganinsa, to shi yana ganinka." Ya ce, "Ba ni labarin alƙiyama." Sai ya ce, "Wanda aka tambaya, bai fi mai tambayar sani ba." Sai ya ce, "Ba ni labarin alamominta." Sai ya ce, "Baiwa ta haifi uwargidanta, kuma ka ga mutane marasa takalma, matsiraita, talakawa, masu kiwon dabbobi, suna tsawaita gine-gine." Sai (mutumin), ya tafi, muka zauna lokaci mai tsawo, sannan sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Ya Umar! Ko ka san mai tambayar nan? Sai na ce, "Allah da Manzonsa su ne suka sani" Sai ya ce, "Haƙiƙa Jibrilu ne ya zo muku don ya koya muku addininku." Muslim ne Ya rawaito shi (#8).


SHARHI

 Wannan hadisi na biyu, an karɓo shi daga Umar ɗan Khaɗɗab. A cikin musulunci Umar ɗan Khaɗɗab shi ne na biyu, mutum na farko shi ne sayyidina Abubakar. Kuma Annabi (ﷺ) ya ce, "Da bayana za a sami Annabi, da ya zamo Umar dan Khaɗɗab."
[Imamu Ahmad da Tirmizi da Hakim suka rawaito shi, Albani ya ce, hadisi ne mai kyau. Duba littafin Albani Silsilatul Ahadisus Sahiha (#327)].
Kuma yana cewa, "A can cikin al‘umman da suka gabata akwai Muhaddasuna-abin da ake nufida Muhaddasuna, wato waɗansu mutane ne da suke da baiwa ta ilhama, waɗanda Allah zai kimsa musu yin wani abu a zuci, sai wannan abin ya dace da shari'ar Allah da ya saukar kan wani Annabi daga cikin Annabawansa. Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "In akwai su a al'ummata, to Umar yana cikinsu." [Imamu Ahmad a cikin Musnad (#339), da Bukhari (#3689) suka rawaito shi]
Dangane da faɗinsa, "....ba a ganin alamun tafiya tare da shi....", alamar tafiya a nan, shi ne a ga gajiyawa tare da shi, in daga nesa yake, sannan a ga ƙura. Babu duk wannan, ga shi kuma ya ce, "....kuma a cikinmu babu wanda ya san shi...." Dukkan abin mamaki ya ƙare a nan wurin. Domin yankin Madina, yanki ne na sahara, in da daga wani ƙauye ya zo, to dole a ga alamar tafiya tare da shi, kamar ƙura, kamar gajiyawa, ko a gan shi da doki, ko alfadari ko rakumi. Amma haka kawai aka ga ya zo, ga tufafmsa fari ƙal, ba abin da ya taɓasu, ga gashin kansa baƙi wuluk, ba alamar tafiya tare da shi, ga shi kuma, "....cikinmu ba wanda ya san shi...." don ba mazaunin Madina ba ne, da mazaunin Madina ne, da mun san shi, saboda mun san kowa. Don kowa ya san kowa a lokacin a Madina,
Dangane da faɗinsa, "....har ya zauna kusa da Annabi (ﷺ) ya jingina gwiwowinsa guda biyu zuwa ga gwiwowinsa, ya ɗora tafukan hannunsa a kan cinyoyinsa....", sai malamai suka yi maganganu daban daban: Waɗansu suka ce wannan baƙon ya ɗora tafukan hannunsa ne a kan cinyoyin Annabi (ﷺ), waɗansu kuma suka ce a‘a! shi bakon ya ɗora hannayensa guda biyu a kan cinyoyinsa, ba a kan cinyoyin Annabi (ﷺ) ba. Wasu sun rinjayar da na ƙarshe saboda shi ne zai fi dacewa da ladabi, kuma shi ne zai fi nuna halin ya kamata. [Duba: Sharhin Sahihi Muslim Na Imam AlNawawi]
Fadin Manzon Allah (ﷺ) cewa"....Ka shaida babu abin bautawa bisa ga cancanta, sai Allah, kuma Muhammad (ﷺ) Manzon Allah ne...." yana nufin ka yarda ba wanda yake cancantar a bauta masa a bayan ƙasa, sai Allah. Ko da an bauta wa wani wanda ba Allah ba, to wannan wanin, bai cancanci bautar ba, an jingina ta ne zuwa ga wanda bai dace da ita ba. Kuma ka yarda babu wanda zai kawo yadda za a yi bautar, sai Annabi Muhammad  (ﷺ). Wannan shi ne ma'anar cewa shi, "....Manzon Allah ne....". Idan ka ɗauki samfurin bauta a wurin wani ba a wurin Annabi (ﷺ) ba, to kamar ba ka yarda da manzancinsa ba ne, ko ka rage wa manzancinsa ƙarfi. Domin dukkan wani abu da yake sunansa ibada ko bauta, wanda za a nemi kusancin Allah da shi, to dole ne ya zama Annabi (ﷺ) ya koyar dashi, in ba Annabi ne (ﷺ)  ya zo da shi ba, kamar an raba aikin Annabi ne an ba wannan mutumin rabi; kamar ana nufin Annabi (ﷺ) bai isar da saƙo gaba ɗaya ba, ya rage wani abu mai falala, bai sanar ba, an sami wani ya zo yanzu yana ƙara wa mutane wani abu. A takaice dai shaidawa Annabi Muhammad (ﷺ) Manzon Allah ne, wannan yana nuna ka bi shi sau-da-ƙafa cikinduk abin da ya zo da shi. Shi ya sa waɗansu malaman suka ce wannan ya ƙunshi ma‘ana ne guda hudu:- Abu na farko: Yi masa ɗa'a cikin duk abin da ya zo da shi, abin da duk ya yi umarni ku bi shi. Abu na biyu: Abin da duk Annabi (ﷺ) ya ba da labari, imma na da, da ya taɓa faruwa, ko abin da zai faru nan gaba a farfajiyar ƙiyama, na labarin wuta da aljannah, dole ne mutum ya gasgata shi, ko abin ya dace da hankalinka, ko bai dace da hankalinka ba, ko abin ya dace da tunaninka, ko abin bai dace da tunaninka ba. Abu na uku: Nisantar duk abin da Annabi (ﷺ)  ya tsawatar, ya ce a rabu da shi. Abu na huɗu: Ka da a bauta wa Allah sai daidai da yadda Annabi (ﷺ) ya zo da shi. To wannan shi ne shaidawa cewa Annabi Muhammad (ﷺ) Manzon Allah ne.
Ma'anar, "....tsayar da sallah...." kuma shi ne sallatar ta a lokacinta, da kiyaye sharuɗɗanta da dokokinta. Sannan kuma mutum ya bayar da zakka ta wajibi. Sannan kuma azumtar Ramadan. Sannan kuma hajji ga wanda ya sami ikon zuwa. Lokacin da Annabi (ﷺ) ya ba shi amsa kan wannan, sai ya ce, "Ka yi gaskiya!" To wannan abin mamaki na biyu kenan, domin abin mamaki na farko, ga wani mutum wanda ba su san shi ba, ga farin tufafi, ga baƙin gashin kai, ba wata alamar tafiya, kuma ba a Madina yake ba, don ba su san shi ba, amma ga shi ya zo wajen Annabi (ﷺ), to daga ina yake? Abu na biyu, galibi idan na yi tambaya, ina yin tambaya ne, don ban san abin ba, amma idan na yi maka tambaya ka amsa, sai na ce "Eh! Ka faɗi gaskiya.", wannan yana nuna na san abin tun kafin in tambaye ka.
A wannan hadisi, Manzon Allah (ﷺ) ya ambaci rukunan imani guda shida: Farko, imani da Allah. Na biyu, imani da Mala‘ikunsa. Na uku, imani da littattafansa. Na huɗu, imani da Manzannin da ya turo. Na biyar, yin imani da ranar tashin alƙiyama. Na shida, imani da ƙaddara. Waɗannan rukunai yadda suke a nan, haka kuma suka zo a cikin ayoyin Alkur'ani, a wani wurin an kawo biyar, a wani wurin kuma an kawo ɗaya 
(Ba musulunci kaɗai shi ne ku juyar da fuskokinku mahudar rana da mafaɗarta ba, musulunci shi ne wanda ya yi imani da Allah da ranar Ƙarshe da Mala'iku da littattafai da Annabawa....) [Baƙara: 177].
 Biyar kenan! saura ɗaya, shi ne can cikin Suratul Ƙamar inda Allah yake cewa,
(Haƙiƙa komai mun halicce shi a kan tsari) [Al-Ƙamar: 49]
Rukunan imani guda shida kenan. Imani da Allah kuma yana da ɓangarori guda uku: Imani da shi ta fuskar Rububiyya, imani da shi da fuskar Uluhiyya, imani da shi ta fuskar Sunaye da Siffofi. Idan ka ce Rububiyya, ka yi imani da Allah ta fuskar ayyukansa, ya kaɗaita a dukkan dangogin aikinsa, kamar kashewa da azurtawa da talautawa da bayar da mulki ko kwacewa da bayar da dukiya ko kwace ta, ko bayar da haihuwa ko hana haihuwa da kawo dare ko kawo rana, da saukar da ruwan sama, da fitar da tsirrai, da bayar da tattalin arzikin ƙasa. Duk waɗannan ayyuka ne na Allah shi kaɗai, babu mai taya shi, domin sama da ƙasa mallakarsa ne, yarda da Allah ta fuskar kaɗaitakarsa a irin waɗannan ayyuka, shi ne yarda da Rububiya.
Na biyu yarda da shi ta fuskar Uluhiyya. Babu wanda za ka bautawa sai shi, dukkan wani dangi na cikin dangogin bauta, haƙƙi ne na Allah shi kaɗai, wani wanda ba Allah ba, ba ya cancanta a bauta masa, wannan ko da Mala‘ika ne, ko da Manzo ne cikin Manzanni, ballantana wanda bai kai darajar Manzanni ba.
Fuska ta uku shi ne, kaɗaita shi ta fuskar sunayensa da siffofinsa. Dukkan sunan da yake sunan Allah ne, to shi kaɗai ya keɓanta da shi, dukkan siffar Allah, shi kaɗai ya keɓanta da ita. Duk abin da ingantaccen hadisi ya tabbatar a matsayin suna na Allah, ko siffa ta Allah, wajibi ne mu yi imani da shi, ba za mu ƙaryata ba, ba za mu karkatar da shi daga ma'anar wannan kalma ba, haka kawai, don ba ta dace da son zuciyarmu ba.
Imani da Mala'iku shi ne imani da su a dunƙule. Akwai wasu siffofl da dukkan Mala'iku sun yi tarayya a kansu, ka yarda da waɗannan siffofin, kamar yadda nassosin Alkur'ani da hadisai suka zo da shi, suka tabbatar. Daga cikin waɗannan, akwai cewa Mala'iku ba a siffata su da cewa maza ne ko mata. Kamar yadda a cikin aljanu akwai maza da mata, Mala'iku ba haka ba ne, su jinsi ɗaya ne babu mata a cikinsu. Siffa ta biyu, mutum ya yarda Mala'iku wata runduna ce mai tarin yawa, wadda babu wanda ya san yawanta sai Allah, Allah ya ce,
(Ba wanda ya san rundunar Ubangijinka sai shi) [Suratul Muddassir: 31].
Siffa ta uku: Ubangiji ya ba wa Mala'iku ƙariln jiki, ya ba su kuma girman halitta. Annabi (ﷺ) ya ce, "Na ga Mala'ika Jibril a daren da aka yi isra'i da ni, a wannan lokaci na gan shi yana da fuffuke ɗaiɗai har guda ɗari shida. [Bukhari (#4857) da Muslim (#174) suka rawaito shi] Kowane fuffuke ɗaya zai iya rufe dukkanin sama, ta yadda in mutum zai ɗaga kansa sama, ba zai iya hango sararin samaniya ba. Abin da yake nuna karfinsu kuwa shi ne an tura Mala'ika ya zo ya ɗauki gari ɗaya, ya tunɓuko shi gaba-ɗaya, ya halakar da gari guda shi kaɗai. Ko Mala'ikan ya yi tsawa, gari guda ya narke, ko al'umma guda ta tafi babu ita. Wannan shi yake nuna ƙarfinsu! Sannan mutum ya yarda cewa, duk inda Mala’iku suke, ba sa saɓa wa Allah.
 (Ba sa saɓa wa Allah a kan duk abin da ya umarce su, kuma suna aikata dukkan abin da aka umarce su) [Suratut Tahrim: 6]
Siffa ta gaba; mutum ya yarda Mala'iku suna bauta ne tsantsa, ba sa saɓo, bauta suke yi dare da rana. Allah ya cece;
 (Suna tsarkake Allah dare da rana ba sa yanke wa) [Suratul Anbiya'i: 20]
Kashi na biyu, shi ne ka yi imani da su tafiran (a rarrabe). Dukkan wanda nassin Alkur'ani ya tabbatar da shi, ko hadisi ya tabbatar da shi, aka faɗe shi da aikinsa, to sai ka yi imani da shi da wannan sunan nasa da aikinsa. Kamar Jibril, sunansa ya zo a cikin Alkur'ani, Mika'il sunansa ya zo a cikin Alkur‘ani, inda Allah yake cewa,
(Duk wanda ya zama maƙiyin Allah da mala'ikunsa da Jibril da Mika'il to Allah maƙiyin kafirai ne) [Suratul Baƙara: 98]
Ka ga a nan, an fadi Jibrila da Mika‘il. Aikin Mala'ika Jibril shi ne kawo wahayi, Mika‘il kuwa aikinsa shi ne koro iskar da take ɗauke da girgije na ruwan sama, da zubo da ruwan saman, da kuma fitar da tsirrai. Sannan akwai mala'ika Israfil, aikinsa shi ne busa cikin ƙaho a ranar tashin Alƙiyama, idan ya yi busa kowa zai mutu, sannan ya sake yin busa a farfaɗo. Allah ya ce,
(Kama aka yi busa a cikin ƙaho, sai duk wanda yake sama da ƙasa ya sume, sai dai wanda Allah ya ga dama, sannan a sake wata busar a cikinsa (ƙahon) sai ga su a tsaitsaye suna jiran tsammani) [Azzumarz 68].

Ya tabbata a cikin hadisi ruwayar Muslim [#769] Annabi (ﷺ) yana yin sallar dare, a cikin sallar daren yana yin addu'ar buɗe sallah, bayan ya yi kabbara, yana cewa, "Ya Allah, Ubangijin Jibrilu da Mika'il da Israfil, mahaliccin sammai da ƙassai...' Sai Mala'ikan mutuwa, wannan sunansa Mala'ikan Mutuwa ko a AIƙur'ani da cikin hadisin Bukhari [#3407] da Muslim [#2372] sunansa Malakul Maut. Hadisin da yake cewa sunansa Azra’ilu bai tabbata ba, hadisi ne mai rauni, don haka sunansa Malakul Maut. Allah yana cewa,
 (Ka ce, "Mala'ikan mutuwa yana ɗaukar ranku wanda aka wakilta gare ku.") [Assajda 11]
 Daga nan sai Malik, Mala'ikan da ke tsaron wuta: Allah ya ce,
(('Yan wuta) suka yi kira, "Ya Malik! Ubangijinka ya kashe mu mana ") [Azzukruf 77]
Daga nan akwai Munkar da Nakir.
To ka ga wannan duk sunayensu ya tabbata ta fuskar nassi. Amma duk Mala'ikan da ba a san sunansa ko aikinsa ba, sai ka yi imani da shi.
Dangane kuwa da imani da littattafan Allah, Allah (SWA) ya ambata mana guda hudu kacal daga cikin littattafan; su ne, Zabura ta Annabi Dawud, Attaura ta Annabi Musa, Injila ta Annabi Isa, sai Alkur'ani na shugaban halitta Annabi Muhammad (ﷺ). Ban da waɗannan, sauran Annabawa dai mun san an ba su littafi, amma ba mu san sunan littafin ba, don nassin Alkur’ani bai faɗa ba, hadisi kuma bai faɗa ba. Idan matambayi ya tambaye ka, "Wane littafi aka ba wa Annabi Shu'aibu?" Sai ka ce, "Ban sani ba!" Wanne aka ba wa Annabi Salihu? Ban sani ba! Wanne aka ba Annabi Hudu? Ban sani ba! Wanne aka ba wa Annabi Nuhu? Ban sani ba! Don Allah bai faɗa ba, Manzonsa bai faɗa ba, ya dai ce ya ba su littafi, sunayensu ba mu sani ba, bai kuma wajabta mana mu sani ba, da ana son mu sani, da an saukar da aya, ko bayani cikin hadisi don mu sani, tunda aka kyale, to ba a so mu sani, sai mu kame bakinmu, tunda wahayi ya riga ya yanke, saboda Annabi (ﷺ) ya bar duniya. Imani da Manzanni kuma ya kasu kashi biyu, imani da Manzanni a jumlace, cewa ba wata al'umma, face sai Allah ya turo mata da Manzo. Allah ya ce,
(Babu wata al'umma, face sai da mai gargadi ya wuce a cikinta). [Faɗir 24]
Wannan yana nuna kulawar Allah ga bayinsa, kada ya bar su sakaka, ba su san makoma ba, sai ya turo musu Manzo. Amma manzannin da aka san sunansu, waɗannan guda ashirin da biyar ne, waɗanda Alƙur'ani ya tabbatar, sauran ba mu san sunayensu ba, ba a kuma kallafa mana mu san sunansu ba. Galibi waɗanda muke samun su a cikin littattafan Isra'ilawa kamar Sham‘ulu da Izƙilu, duk wannan Isra'illiyat ne. Amma in ka duba a cikin Alƙur'ani, an kawo maka sunayen Manzanni, an kawo maka goma sha takwas a jere a cikin suratul An'am [83-86] inda Allah yake cewa,
(Waccan hujjarmu ce muka bai wa Ibrahim a kan mutanensa, muna ɗaukaka darajojin waɗanda muka ga dama. Haƙiƙa Ubangijinka mai hikima ne Masani. Mun ba (Annabi Ibrahim) kyautar Ishaƙa da Yaƙub, dukkansu mun shiryar da su, haka ma Nuhu mun shiryar da shi tun kafin su. Daga zuriyar (Ibrahim akwai) Dawud da Sulaimanu da Ayyub da Yusuf da Musa da Haruna, haka nan muka saka wa masu kyautatawa. Da Zakariyya da Yahya da Isa da Ilyas, dukkaninsu salihai ne. Da Isma'il Da Alyasa‘a da Yunusu da Luɗ, dukkaninsu mun fifita su a kan talikai). [Al-an'am: 83-86]
Sha takwas kenan a nan a jere, sauran kuma ka je ka neme su a wasu wuraren daban a cikin Alƙur'ani Mai girma.
Shi kuwa imani da ranar tashin alƙiyama, yana nufin imani da ranar da idan ta zo, za a yi sakamako ga bayi, za a ƙididdige ayyukan bayi, za a yi sakamako da aljanna, ga wanda ya yi wa Allah biyayya, za a yi sakamako da gidan wuta, ga wanda ya saɓa wa Allah Ta'ala.
Shi kuma imani da ƙaddara ya ƙunshi abubuwa ne guda huɗu, wanɗanda in ka yi imani da su a dunule, su ne za su bayar ka yi imani da ƙaddara. Abu na farko, ilimi: cewa Ubangijin Ta'ala ya san dukkanin halittunsa da ayyukansu da inda za su zauna, da kwanakin da za su yi, da sana'o'in da za su yi, tun kafin halittar su, ya san da wannan abu. Na biyu, Ubangiji ya rubuta duk kaikawon da halittu za su yi, ayyukansu, soja da ɗan sanda, da ɗan kasuwa, da malami da ɗan makaranta, wannan tun kafin a halicci duniya da shekara dubu hamsin, Allah ya rubuta wannan ya ajiye, kamar yadda hadisi ya nuna. Abu na uku, ba abin da zai faru a cikin duniyar nan na mutuwa ko na rayuwa, ko na ɗaukaka ko na ƙaskanci, na cuta ko na lafiya, face sai Allah ya ga damar faruwarsa,.domin mulkin Allah ya sha bamban da mulkin sauran jama'a. Abu na huɗu, Ubangiji (SWA) shi ya halicci ayyukanmu tun kafin mu. Ma'ana duk abin da mutum zai aiwatar na dangin alheri ko kishiyar alheri, Ubangiji (SWA) ne ya halicci wannan abin, sai dai kai ɗan Adam kana da zaɓi na ka yi alheri ko ka yi sharri. Allah ya ce,
(Mun shiryar da shi (mutum) hanya, ko dai ya zama mai godiya (ga Allah, wato ya bauta masa) ko kuma ya zama mai yawan kafirci) [Al Insan: 3]
Ba ka kafa hujja ranar tashin alƙiyama ka ce, ai Allah ya riga ya ƙaddara zan yi kaza, tun lokaci kaza, don haka in ya so in yi ɗa'a, ɗa'ar zan yi, in ya so in yi saɓo, shi ne ya ga dama, ni ba ni da zaɓi. Ba za ka ce wannan ba! Don kuwa duk wanda ya ce wannan, to ka ce ya sami bene mai hawa biyu, ka ɗaura masa tsani ya tattaka ya hau. Idan ya hau, sai ka cire tsanin, ka ce to sauko ba tsanin, idan Allah ya ga dama ka karye, in ya ga dama ka sauka lafiya. Ko shakka babu, ba zai yarda da wannan ba. Dole sai ka kawo tsani, ko lifta! To don me zai ƙi bauta wa Allah kuma da kansa ya yi saɓo, ya ce wai Allah ne ya ga dama ya yi. To don haka imani da ƙaddara shi ne imani da waɗannan abubuwa, cewa lallai Ubangiji (SWA) ya rubuta haka, kuma Ubangiji ganin damarsa ne abin da duk ke faruwa a gidan duniya, kuma Ubangiji shi ne ya halicce mu da kuma ayyukanmu gaba ɗaya. Sannan wajen imani da ƙaddara ba a jingina wa Allah (SWA) sharri, kowane lokaci ana jingina wa Allah alheri ne. Alheri da kishiyarsa ɗin duk daga Allah suke, sai dai shi Allah ba a jingina masa sharri, saboda duk abin da Allah ya halitta, babu sharri tsantsa, sai .dai a wurin ɗan Adam, amma ta fuskar Ubangiji (SWA) abun ba sharri ba ne. Yanzu shi ɗan Adam idan aka ɗora masa ciwon kai, ta iya yiwuwa ya fuskance shi a matsayin sharri, amma kuma ya tabbata a cikin hadisi, duk wanda aka ɗora wa wata cuta ko ƙaya mutum ya taka, za ta kankare masa zunubansa. Wannan alheri ne, amma duk da haka ba za ka so ka wuni ka kwana kana zazzaɓi ko kana ciwon kai ba, saboda kai a gare ka sharri ne, amma a wajen Ubangiji alheri ne. Don haka ba a jingina wa Allah sharri, saboda duk abin da ya halitta akwai wani alheri a ɓoye wanda shi ɗan Adam ba zai gano shi ba.
Daga can kuma, dangane da kyautatawa, sai ya ce, shi ne "Ka bauta wa Allah kamar kana ganinsa, don in ba ka ganinsa, to shi yana ganinka...." a wata riwayar, "Ka tsoraci Allah kamar ga shi kana ganinsa a gabanka zai kama ka da azaba in ka saɓa masa."
Waɗannan su ne abubuwa guda uku da Annabi (ﷺ) ya zana a cikin wannan hadisin. Abu na farko Al-Islam. Abu na biyu Al-Iman. Abu na uku Al-Ihsan.
Sai kuma ya ce, "Ba ni labarin alƙiyama." Sai Annabi (ﷺ) ya ce da shi, "Wanda aka tambaya, bai fi mai tambayar sani ba." Abin da yake nufi, shi ne bai san tashin alƙiyama ba, domin sanin tashin alƙiyama al'amari ne da Allah ya keɓanta da shi. Allah shi ya keɓanta sanin yaushe alƙiyama za ta tsaya, ya dai tabbata cikin hadisi cewa ranar juma'a ne za a tashi alƙiyama, amma wacce juma'ar, mai zuwa ko waccan ta gaba, Allahu A'alam! Allah ne kawai ya san wacce juma'a ce. Saboda haka ba wanda ya san ranar da za a tashi alƙiyama, sai Allah.
Dangane da cewa, "Baiwa ta haifi Uwargidanta....", malamai sun yi bayani suka ce, abin da ake nufi da wannan shi ne, musulunci zai haɓaka a buɗe garuruwa, a ci su da yaƙi, a kama kuyangi mata da yawa. Idan mutum ya zo ya auri baiwa ya yi saɗaka da ita, sai ta haihu, ɗan data haifa ɗa ne, ita kuma ta zama baiwa, shi ne abin da wasu malaman suka fassara wannan. [Don ƙarin bayani duba "Fathul Bari" na Imam Ibnu Hajar J. 1 sh. 122 da "Sharhin Muslim" na Imam An-Nawawi j. 1 sh. 132]

Sai kuma ya ci gaba da bayanin alamominta, ya ce, za ka ga mutanen da ƙafarsu ba takalmi, ga su babu tufafin kirki, ga su kuma masu kiwon awaki, za ka ga irin waɗannan mutane daga ƙarshe sun zo suna gasar tsawaitawa wajen gini; wannan yana so
katangarsa ta fi ta wane! In ka ga irin wannan ta faru, to ƙiyama ta kusa zuwa kenan.
Bayan wannan mutum ya gama tambayar Annabi (ﷺ), shi kuma ya ba shi wannan amsa, sai ya tashi ya tafi. Umar ya ce, "....muka zauna lokaci mai tsawo...." sannan sai ya ce da ni, "Ya Umar! ko ka san mai tambayar nan?" Sai na ce, "Allah da Manzonsa ne suka sani." Sai ya ce, "Haƙiƙa Jibrilu me ya zo, don ya koya muku addininku." Ma'ana, Mala'ika Jibrilu ya yi tambaya, ba don shi ba, sai don ku, ku fahimci menene musulunci, ku fahimci ihsani, ku gane alamomin tashin alƙiyama. Don ku ya yi tambayar, don ku sani. Shi ya sa tambaya da amsa, ɗaya ce daga sigogi na yada ilimi tsakanin al‘umma, shi ya sa Alƙur'ani ya zo da ita da yawa, kuma shi ya sa a hadisin Annabi (ﷺ) da dama za ka ga alamar tambaya da yawa, sannan amsar ta zo. To wannan ruwayar haka take, Imamu Muslim ya rawaito.
A wata riwayar da Tirmizi ya rawaito [#2610] a maimakon a faɗi Al-Islam kafin a faɗi Al-Iman sai aka faɗi Al-Iman, sannan aka ambaci Al-Islam daga baya. A wata riwayar daban kuma a wani wurin daga cikin inda Muslim ya rawaito, da aka ambaci Al-Islam ba a kawo Imani ba, sai aka kawo Al-Ihasan, sannan daga ƙarshe aka kawo Al-Iman. Dukkaninsu dai waɗannan abubuwa guda uku mataki-mataki ne daga cikin matakan musulunci. A nan wurin an fassara mana musulunci da ayyukan gaɓɓai ne, kalmar shahada harshe ne ke furta wannan, gaɓɓai ne ke yin salla, zakka, azumi, hajji. Waɗannan ayyuka kuma sun kasu kashi uku: Akwai wanda ake yi da jiki kaɗai, akwai kuma waɗanda ak yi da dukiya kaɗai, akwai kuma na dukiya da gangar jiki. Kalmar shahada harshe k furta ta, sallah gangar jiki ce ke yi, azumi gangar jiki ke yi, wanda ake yi da dukiya kaɗai shi ne zakka ta wajibi, wanda kuma aka haɗa wani ɓangare na dukiya da jiki shi ne aikin hajji, sai ya kasance an mamaye dukkan ayyukan na zahiri. Domin dukkan wani aiki ko dai da gangar jiki da dukiya, ko da dukiya kadai, ko da gangar jiki kaɗai, in dai ayyukan ibada ne. A nan an fassara musulunci da cewa ayyukan zahiri, da aka zo fassara imani, sai aka ambaci dukkan abin da yake ƙuduri na zuci kaɗai, shi ya sa sai wadansu malamai ke cewa, lokacin da duk aka haɗa musulunci da imani a cikin hadisi ko aya, to Islam yana nufin ayyukan zahiri', Al-Iman yana nufin ƙudiri na zuci, to Al-Ihasan shi ne shugaban gaba ɗaya.



(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN MARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...